Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kafin hakan Amir-Abdollahian ya ziyarci kasashen Rasha da Lebanon inda ya gana da jami’an kasashen biyu.
A ziyarar farko da ya kai Lebanon a matsayin Ministan Harkokin Wajen Iran, Amir-Abdollahian ya gana da Shugaba Michel Aoun, Kakakin da Majalisar dokokin kasar Nabih Berri, da Firaminista Najib Mikati, da Ministan Harkokin Waje Abdullah Bouhabib kuma sun tattauna kan batutuwan da suka shafi yankin da na kasashen biyu.
Da yake jaddada gagarumin goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga Lebanon, ministan harkokin wajen na Iran ya sanar da shirye -shiryen gwamnati na bayar da cikakken tallafi.
Kafin isa Beirut, Amir-Abdollahian ya gana da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov, a Moscow.
342/